An Karrama Gwamnan Jigawa Kan Habaka Noma
Cibiyar masana hulda da jama’a ta Najeriya (NIPR) ta yi taron karrama gwamannan jihar Jigawa Malam Umar A. Namadi da lambar yabo mafi girma ta cibiyar (DIAMOND PRIZE) bisa zamowarsa gwarzon gwamna a fannin habbaka aikin noma da samar da abinci.