An karrama Muhammad Babandede, OFR, OCM, da wasu kungiyoyi kan aiyukan jin kai ga marasa galihu.
Ma’aikatar jin kai da rage talauci ta Nijeriya, tare da kungiyar aiwatar da jin kai ta kasa Nigeria Humanitrian Action, ta karrama tsohon shugaban hukumar shige da fice ta Nijeriya, Muhammad Babandede, OFR, OCM, mai ritaya, tare da wasu kamfanoni, bisa irin gudummawar da suke bayarwa wajen tallafa wa al’umma ta hanyar aiyukan jin kai. […]