An karrama Muhammad Babandede, OFR, OCM, da wasu kungiyoyi kan aiyukan jin kai ga marasa galihu.

Ma’aikatar jin kai da rage talauci ta Nijeriya, tare da kungiyar aiwatar da jin kai ta kasa Nigeria Humanitrian Action, ta karrama tsohon shugaban hukumar shige da fice ta Nijeriya, Muhammad Babandede, OFR, OCM, mai ritaya, tare da wasu kamfanoni, bisa irin gudummawar da suke bayarwa wajen tallafa wa al’umma ta hanyar aiyukan jin kai.

A ranar 19 ga watan Agusta na kowacce shekara, majalisar dinkin duniya ta ware domin bikin ranar jin kai ta Duniya, inda ake tunawa da ma’aikatan jin kai da suka rasa rayukansu yayin gudanar da aiyukan taimakon bil’adama.

A yayin bikin, an yaba wa wadanda aka karrama bisa irin gudummawar da suke bayarwa wajen tallafa wa marasa galihu da kuma inganta rayuwar al’umma ta hanyar ayyukan jin kai.

Daraktan tsare-tsare na gidauniyar SURE 4U, Kwantirola Munnir Yari, mai ritaya, wanda ya wakilci Muhammad Babandede, OFR, OCM, a wajen bikin karramawar, ya bayyana cewa an ba shi lambar yabon ne sakamakon irin taimakon jin kai da yake bayarwa ga talakawa, musamman ta hanyar gidauniyar SURE 4U.

Munnir Yari, ya kara da cewa kungiyar ta gudanar da bincike da bibiyar ayyukan da gidauniyar SURE 4U ke gudanarwa wajen tallafa wa marasa galihu, musamman a Abuja, Jigawa, Kano da Katsina, da sauran wurare, kafin ta yanke shawarar bayar da lambar yabon.

Sauran wadanda aka karrama sun hada da gidauniyar Dangote, gidauniyar MTN, gidauniyar T.Y. Danjuma da Access Bank, bisa irin gudummawar da suke bayarwa wajen ayyukan jin kai da tallafa wa al’umma.

An gudanar da taron ne a Abuja Continental Hotel, a cikin ɗakin taro na Ladi Kwali, inda mahalarta daga bangarori daban-daban suka halarta.

 

Post masu alaƙa

An gabatar da jirage marasa matuƙa na ARCO Worldwide Services Limited domin ƙarfafa aiyukan tsaro a Arewa maso Yammancin Nijeriya.

Malaman KASU kimanin 200 ne suka bar jami’ar – ASUU

Babu shugaban da ya sauya tarihin Najeriya kamar Babangida — Tinubu