Gwamnan Kano ya naɗa Barista Hafsat Kutama shugabar hukumar PCACC
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya naɗa Barista Hafsat Ada’u Kutama a matsayin shugabar riƙo ta Hukumar Karɓar Korafe-korafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (PCACC) ta Jihar Kano. Naɗin ya biyo bayan murabus da shugaban hukumar ta PCACC, Saidu Yahaya, ya yi a ranar Talata. Rahotanni dai na cewa Saidu Yahaya ya […]