Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya naɗa Barista Hafsat Ada’u Kutama a matsayin shugabar riƙo ta Hukumar Karɓar Korafe-korafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (PCACC) ta Jihar Kano.
Naɗin ya biyo bayan murabus da shugaban hukumar ta PCACC, Saidu Yahaya, ya yi a ranar Talata.
Rahotanni dai na cewa Saidu Yahaya ya miƙa wasiƙar murabus ne bayan fuskantar matsin lamba daga Gwamnatin Jihar Kano kan rashin cika wasu daga cikin abubuwan da ake sa ran zai aiwatar a yayin gudanar da aikinsa.
An naɗa Saidu Yahaya a matsayin shugaban hukumar ne a watan Agustan shekarar 2025, bayan karewar wa’adin tsohon shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado.
Sabuwar shugabar riƙon ƙwaryar, Barista Hafsat Kutama ta yi karatun Shariʼa a Jamiʼar Bayero, kuma ta yi aiki da Maʼaikatar Shariʼa ta Kano, kafin bisani ta koma aiki a hukumar ta PCACC, inda gwamnan Kano ya naɗa ta a matsayin sakatariyar hukumar a watan Agustan 2025.