Matsin Tattalin Arziki Ya Jefa ‘Yan Najeriya Miliyan 130 Cikin Baƙin Talauci – SMEDAN
Shugaban Hukumar Raya Kanana da Matsakaitan Masana’antu a Najeriya (SMEDAN), reshenKaduna, Alhaji Badamasi Barau, ya ce matsin tattalin arzikin da ake fuskanta a kasar nan ya jefa sama da mutane miliyan 130 cikin talauci.