Matsin Tattalin Arziki Ya Jefa ‘Yan Najeriya Miliyan 130 Cikin Baƙin Talauci – SMEDAN

Shugaban Hukumar Raya Kanana da Matsakaitan Masana’antu a Najeriya (SMEDAN), reshen Kaduna, Alhaji Badamasi Barau, ya ce matsin tattalin arzikin da ake fuskanta a kasar nan ya jefa sama da mutane miliyan 130 cikin talauci.
Alhaji Badamasi Barau ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da kasida a wurin taron Ranar Albarkatun Ƙasa karo na 21 da Cibiyar Samar da kayayyakin Ta Ƙasa (NPC) ta shirya a Kaduna.
Badamasi Barau ya bukaci jama’a da su kara kaimi a harkokinsu na yau da kullum domin shawo kan matsalar tattalin arziki.
Ya ce, “Akwai bukatar a shawo kan kalubalen tattalin arzikin da ya jefa mutane sama da miliyan 130 cikin talauci a Najeriya.
“Yana da kyau mutane su kara kaimi a harkokinsu na yau da kullum domin tsamo kai daga matsalar tattalin arzikin da ƙasar nan ke ciki.
“Taken taron na bana ya dace da halin da ake ciki, la’akari da ƙalubalen da ake fuskanta a yanzu”.
A jawabin maraba, Kodinetan Hukumar NPC na Jihar Kaduna, Mista Gideon Malgwui, ya ba da tabbacin cewa cibiyar tana iya bakin ƙoƙarinta wurin samar da ci gaba mai ɗorewa a tsakanin jama’a, ta hanyar ayyukanta na yau da kullum.
Koodinentan ya yi fatan cewa wannan taro zai tasiri mai nisa wajen nemo mafita ga galibin matsalolin da ke da alaka da tattalin arziki.
Kazalika, wadanda suka yi tattauna akan jawabin babban baƙon, Alhaji Kabiru Kasim da Mohammed Aminu Yahaya, sun yi tsokaci kan bukatar ‘yan Nijeriya su samar da hanyoyin da za a bi domin samun rayuwa mai inganci.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda