Dambarwar Wike da soja: Ba Za Mu Bari A Cutar Da Wanda Yake Yin Aikin Da Ya Kamata Ba: Badaru
Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya tabbatar da cewa gwamnati tare da manyan hafsoshin rundunonin tsaro za su kare duk wani soja da yake kan aikin sa bisa doka. Badaru ya bayar da wannan tabbaci ne yayin da yake amsa tambayoyin ’yan jarida a taron manema labarai na ma’aikatar, wanda aka shirya don bikin tunawa […]