Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya tabbatar da cewa gwamnati tare da manyan hafsoshin rundunonin tsaro za su kare duk wani soja da yake kan aikin sa bisa doka.
Badaru ya bayar da wannan tabbaci ne yayin da yake amsa tambayoyin ’yan jarida a taron manema labarai na ma’aikatar, wanda aka shirya don bikin tunawa da sojoji da suka mutu wajen kare kasa (Armed Forces Remembrance Celebration and Remembrance Day) na shekarar 2026, a ranar Laraba a Abuja.
Wannan magana ta fito ne bayan takaddama da ta barke a ranar Talata tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyeson Wike, da wani Laftanar na Rundunar Sojan Ruwa, kan wata gona da ke Abuja, wadda ake zargin mallakar tsohon Babban Hafsan Sojan Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo ce.
Badaru ya ce: “To, a ma’aikatar mu, da kuma a cikin rundunonin tsaro gaba ɗaya, za mu ci gaba da kare jami’an mu da suke kan aikin su bisa doka.
“Mun fara bincike a kan wannan lamari, kuma muna tabbatarwa cewa duk jami’in da yake aikinsa bisa doka zai samu cikakken kariya.
“Ba za mu yarda a cutar da shi ba muddin yana gudanar da aikinsa yadda ya kamata, kuma muna alfahari da yadda yake aikin nasa,” in ji shi.