Nan ba da jimawa ba za a biya diyya ga mafarautan Kano da aka kashe a Uromi — Gwamnatin Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ana kan shirin kammala tattaunawa domin biyan diyya ga mafarautan jihar da aka kashe a wani hari da ya faru a Jihar Edo a bara. Wannan bayani ya fito ne daga bakin Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida , Ibrahim Abdullahi Waiya, yayin wata ziyarar jaje da tawagar gwamnati […]