Nan ba da jimawa ba za a biya diyya ga mafarautan Kano da aka kashe a Uromi — Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ana kan shirin kammala tattaunawa domin biyan diyya ga mafarautan jihar da aka kashe a wani hari da ya faru a Jihar Edo a bara.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida , Ibrahim Abdullahi Waiya, yayin wata ziyarar jaje da tawagar gwamnati ta kai fadar Hakimin Bunkure domin jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Ya ce ziyarar na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na nuna tausayi da goyon baya ga iyalan mamatan, wadanda aka kashe yayin da suke dawowa gida domin gudanar da bikin Sallah.

A cewarsa, gwamnatin Kano na ci gaba da tuntuba da gwamnatin Jihar Edo domin tabbatar da cewa an biya diyya ga wadanda abin ya shafa, yana mai cewa ana sa ran cimma matsaya cikin kankanin lokaci.

Waiya ya kara da cewa tun da farko Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da bayar da tallafin kudi da kayan abinci ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su.

Ya ce iyalan mutum 16 da aka kashe sun samu Naira dubu 300 kowannensu, yayin da mutum 13 da suka jikkata suka karbi Naira dubu 200 kowannensu. Haka kuma, an bai wa kowane daga cikinsu buhunan shinkafa guda biyu domin rage musu radadin halin da suke ciki.

Kwamishinan ya bayyana cewa wannan tallafi na daga cikin matakan da gwamnati ke dauka na rage wahalhalu da radadin da iyalan ke ciki, duk da jinkirin da aka samu a baya sakamakon wasu matsalolin gudanarwa.

Ya kuma bukaci iyalan da su kara hakuri, yana mai tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da kula da jin dadinsu, ciki har da tallafa wa ‘ya’yan wadanda suka rasu.

A nasa bangaren, Hakimin Bunkure, Aminu Isah Umar, ya yaba da wannan mataki na gwamnatin Kano, yana mai cewa tallafin zai taimaka matuka wajen rage wahalhalun da iyalan ke fuskanta.

 

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda