Masu Ruwa Da Tsaki A Unguwar Sharada Sun Amince Da Dokoki 29 Don Gyara Tarbiya.
Al’ummar unguwar Sharada da ke cikin ƙaramar hukumar Birni a jihar Kano, sun bijiro da wasu dokoki 29 domin tsaftace halayyar mutane da tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyinsu. Daga ciki dokokin akwai dokar hana zance ko hirar dare tsakanin sauraryi da budurwa da ma hana zance a cikin mota sannan ka da masoya su […]