Masu Ruwa Da Tsaki A Unguwar Sharada Sun Amince Da Dokoki 29 Don Gyara Tarbiya.

Al’ummar unguwar Sharada da ke cikin ƙaramar hukumar Birni a jihar Kano, sun bijiro da wasu dokoki 29 domin tsaftace halayyar mutane da tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyinsu.

Daga ciki dokokin akwai dokar hana zance ko hirar dare tsakanin sauraryi da budurwa da ma hana zance a cikin mota sannan ka da masoya su wuce ƙarfe 10 dare suna zance.

Wannan matakin, a cewar mahukuntan yankin, ya fito ne sakamakon damuwar da ake fuskanta kan taɓarɓarewar tarbiyya da ƙaruwar matsalolin tsaro, da kuma rashin bin ƙa’idojin al’ada a tsakanin matasa masu neman aure.

Post masu alaƙa

Kwamitin zaman lafiya ya gana da yan sandan Kano kan zaɓen 2027.

An kashe kwamandojin ’yan bindiga biyu a Katsina

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi