Home » Taron KILAF Zai Hada Jama’a Daga Kasashe 66 A Kano

Taron KILAF Zai Hada Jama’a Daga Kasashe 66 A Kano

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

A ranar 25 ga watan Nuwamba na shekarar 2024 ake sa ran za a fara gudanar da bikin Kasuwar Fina-Finai ta Kano (KILAF) karo na 7, inda ake sa ran kasashe sama da 66 halarta.

Ana sa ran Farfesa Emmanuel Emasealu ne zai jagoranci taron na bana.

Kawo yanzu kwamitin tsare-tsaren bikin sun fitar da jerin sunayen fina-finan da aka zaba domin karramawa a bikin.

Abdulkareem Mohammed, babban jami’in gudanarwar na KILAF ya bayyana wadannan shirye-shiryen ne yayin wata ganawa da manema labarai a cibiyar ‘yan jarida ta Kano.

Kawo yanzu an turo fina-finai 510 daga kasashe 66 na duniya, inda 430 suka fito daga kasashen Afirka 35. A cikin waɗannan, an zaɓi fina-finai 57 daga ƙasashe 16 don gasar Fim ta KILAF ’24 na nau’ika 17.

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ne zai shugabanci liyafar maraba a taron da zai dauki kwanaki biyar ana gudanarwa a jihar.

Alh Abdulkarim Muhammad ya bayyana cewa sun kirkiro gasar bunkasa harshen Hausa da sauran harsunan Africa da za,a yi shirya fina-finai, tare da bayar da ilimi na musamman ga masu shirya wasan kwaikwayo, dama masu magana d harshen Hausa a Duniya.

“Ya kara da cewa bunkasa harsunan Africa zai sa, kowa ya kara himma wajen martaba yaran sa Al’adun sa, da kare martabar fina-finai a Duniya, ta yadda harsunan zasuyi gogayya da sauran harsuna”.

Abdulkarim Muhammad ya ce gasar fina-finan ta kilaf za,a gudanar da ita a Jihar Kano, da ake saran Shigowar Baki daga kasashen afrika dama nahiyar Turai zasu zo, kuma hakan zai bunkasa tattalin arzikin Jihar kano da Kasa baki daya.

Rahoto Sani Abdurrazak Darma

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?