• Home  
  • Tinubu Ya Naɗa Sabon Minista
- Babban Labari - Labarai

Tinubu Ya Naɗa Sabon Minista

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Dokta Bernard Mohammed Doro daga Jihar Filato a matsayin sabon Minista a gwamnatinsa. Mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da fitar a wannan Talatar, inda ya ce naɗin zai tabbata ne bayan amincewar Majalisar Dattawa. Gwamnatin Tarayya Ta Ce EFCC Ta […]

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Dokta Bernard Mohammed Doro daga Jihar Filato a matsayin sabon Minista a gwamnatinsa.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da fitar a wannan Talatar, inda ya ce naɗin zai tabbata ne bayan amincewar Majalisar Dattawa.

Naɗin Dokta Doro na zuwa ne bayan zaben Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda da aka yi a matsayin Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa a watan Yuli, wanda a baya yake riƙe da muƙamin Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci.

Kazalika, sanarwar ta ce tuni an miƙa wa Majalisar Dattawa sunan sabon ministan domin tantancewa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000