Tsohon shugaban Hukumar Tara Haraji ta Ƙasa (FIRS), Muhammad Nami, ya yi martani a kan sallamarsa da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba sannan ya naɗa mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin kuɗaɗen shiga, Zacchaeus Adedeji, a matsayin muƙaddashin shugaban hukumar harajin wato shugaban riƙo kafin a tabbatar da shi a muƙamin.
Wasu ƴan awanni bayan sallamarsa, Mohammad Nami, mai shekaru 55 a duniya ya fitar da sanarwa inda ya yi godiya ga tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan ba shi damar hidimtawa ƙasa. Haka kuma Nami ya miƙa godiyarsa ga ma’aikatan Hukumar ta FIRS waɗanda suka yi aiki tare da shi tsawon shekaru.
Har wa yau Muhammad Nami ya ƙara jaddada nasarorin da hukumar ta samu a ƙarƙashin jagorancinsa inda yace bisa kulawarsa Hukumar ta tara Naira tiriliyan 8 cikin watanni takwas, kuma yace nan zuwa ƙarshen shekara za a ga sabon tarihin da ya kafa na tara aƙalla Naira tiriliyan 13 a Hukumar.
Nami ya ce zai bar hukumar ta tara haraji a matsayin wanda burinsa ya cika bayan ya cimma duk abubuwan da ya sa gaba na inganta tsarin aikin Hukumar ya dace da na sauran ƙasashen duniya.