Dubun wasu sun cafke wasu masu safarar makamai ɗauke da harsashi 314 ta cika a Jihar Kogi.
Dakarun Rundunar Sojojin Najeriya ta Birgeet ta 12 sun kama mutane biyu da ake zargin masu safarar kayan a cikin wata motar haya.
Muƙaddashin kakakin rundunar, Laftanar Hassan Abdullahi, ya sanar da cewa an gudanar da aikin ne a ranar 20 ga Afrilu, 2026, bayan samun sahihin bayani kan motsin wasu da ake zargin suna safarar kayan ta’addanci ne a yankin da rundunar ke da alhakin tsaro
Sojojin sun tare wata motar bas kirar Toyota da ke kan hanyar Obajana daga Makurɗi, inda bincike ya kai ga cafke Mallam Zubairu Abubakar da Adamu Abubakar Abdullahi.
A cikin motar, sojojin sun gano buhun da ke ɗauke da harsasai 314 na bindiga kirar AK-47 da aka ɓoye a bayan kujerar direba. Haka kuma an kwace wayoyi biyu, lasisin tuƙi, katin shaida na NIN da wani katin shaida.
An mika waɗanda aka kama da kayan da aka ƙwace ga Rundunar Sashen Binciken Sojoji na 12 domin ci gaba da bincike.
A wani labari mai alaƙa, rundunar ta ce a ranar 29 ga Maris, 2026, sojojin da ke sintiri a hanyar Jamata–Owara, sun kama wani mai babur da ake zargin mai safarar kayan ta’addanci ne.
Binciken ya gano cewa babur ɗin an yi masa gyara na musamman domin ɓoye harsasai da sauran kayan aiki.
Wannan bincike ya kai ga gano alaƙarsa da wasu manyan ’yan ta’adda, inda daga bisani aka cafke wani fitaccen mai safarar makamai, Mathew Elisha wanda aka fi sani da Nasara, wanda tun da farko ke cikin jerin wadanda jami’an tsaro ke nema.
