• Home  
  • Uba Sani ya ɗauki Jerry Adams mataimakinsa a Zaɓen 2027
- Siyasa

Uba Sani ya ɗauki Jerry Adams mataimakinsa a Zaɓen 2027

Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, ya sanar da ɗaukar Jerry Adams a matsayin mataimakinsa a Zaɓen 2027, bisa shawarwari da addu’o’i da ya ce sun jagoranci wannan mataki. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da gwamnan ya fitar a shafinsa na X a yammacin wannan Talatar. Uba Sani ya ce ɗaukar Jerry Adams […]

Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, ya sanar da ɗaukar Jerry Adams a matsayin mataimakinsa a Zaɓen 2027, bisa shawarwari da addu’o’i da ya ce sun jagoranci wannan mataki.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da gwamnan ya fitar a shafinsa na X a yammacin wannan Talatar.

Uba Sani ya ce ɗaukar Jerry Adams ya yi daidai da manufar gwamnatinsa ta haɗin kai, adalci da bai wa kowane ɗan jihar damar jin yana da muhimmanci a harkokin gwamnati, ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi ƙoƙarin tabbatar da ci gaba a dukkan ƙananan hukumomin jihar da kuma ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al’ummomi.

Gwamnan ya yaba wa Jerry Adams a matsayin gogaggen jami’in gwamnati kuma ƙwararren mai kula da harkokin haraji.

Kazalika, ya bayyana cewa Jerry Adams mutum ne mai gaskiya, ƙwazo da kishin zaman lafiya, wanda zai taimaka wajen ci gaba da gina Kaduna mai haɗin kai da ci gaba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000