Akalla mutum biyu sun mutu sakamakon ruftawar wani bene mai hawa biyu a unguwar Garki da ke tsakiyar birnin tarayyar Najeriya Abuja.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na birnin Abuja, Abbas Idris, ya tabbatar wa da manema labarai kan faruwar al’amarin, inda ya ce jami’an su na ci gaba da aikin ceto a wurin da lamarin ya faru.
Abbas Idris ya ce kawo yanzu an zaƙulo mutane 37 daga cikin ginin, inda mutum biyu suka mutu, sannan an garzaya da wasu 35 zuwa asibiti.
Tuni jami’an ceto daga hukumomin bayar da agajin gaggawa na FEMA, da jami’an kashe gobara da haɗin gwiwar jami’an kiyaye aukuwar haɗura ta ƙasar, FRSC suka isa wurin domin tabbatar da aikin ceto waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin ginin.
Kawo yanzu dai hukumomin ba su bayyana abin da ya haddasa ruftawar ginin ba.