Akalla lauyoyi 60 ne suka garzaya wata babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya domin shigar da kara kan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) saboda kin sakin Emefiele.
Lauyoyin sun ce karar na da nasaba da cin zarafin wasu hukunce-hukuncen da kotun ta umarci hukumar ta saki tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Lauyoyin da Mista Maxwell Opara da Ahmed Tijani suka jagoranta, sun roki kotun da ta kai wasu manyan jami’an DSS gidan yari har sai an sallami Emefiele.
Lauyoyin sun ce bisa hukunci da mai shari’a M. A. Hassan da Hamza Muazu da kuma mai shari’a Bello Kawu suka yanke, ya kamata Darakta-Janar na DSS, Yusuf Magaji Bishi, ya saki Emefiele.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan shigar da karar, Opara ya ce kungiyar za ta bi diddigin lamarin har zuwa karshe sannan kuma ta tabbatar da cewa an tura Darakta-Janar na DSS, Bichi zuwa gidan yari.