Tun bayan da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta shiga rikicin rashin nasara a ‘yan makonnin nan musamman a gasar Laliga masana suka fara nazari da bayyana kamanceceniya.
Kamanceceniyar kuwa a tsakanin tsohon mai horas da kungiyar wato Xavi da kuma mai horas wa na yanzu Hansi Flick.
Barcelona dai ana ganin a farkon kakar wasa tana jefa kwallaye guda 4 ko 5 a ragar aboknan wasanta, ciki har da wasan da ta lallasa Real Madrid daci 4 – 0 har gida.
Hakan ya sanya ake ganin an samu gagarumin sauyi a Barcelona inda ake ganin Laliga ta zama ta Barcelona ganin yadda abokiyar hamayyars su Madrid take samun tasgaro.
Saidai kuma a wasanni guda 3 na baya bayannan da Barcelona ta fafata batasamu nasara a ko guda daya ba inda tayi rashin nasara a wasanni biyu a hannun Real Sociedad da Las Pamas ta buga kunnen doki da Celta Vigo.
Hakan ya sanya Real Madrid take neman taras da ita, inda idan Madrid ta ci kwantan wasanta to ta tserewa Barcelona da maki 2.
Abin da yasa magoya bayan Barcelona da wasu masana suke hangen duk kanwar ja ce ko gara jiya da yau, kakar wasan da ta gabata a karkashin Xavi lokacin da Barcelona ta fafata wasanni 15 to maki 34 da tara. Haka ma yanzu duk da an samu sauyi a wasanni 15 maki 34 ta ajiye a karkashin sabon mai horas wa.
Haka zalika a daren Yau Barcelona za ta fafata da Mallorca, matukar Barcelona ta sake yin rashin nasara to ta tabbata gara jiya da yau.

