Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce kungiyar ‘yan ta’addar Lakurawa ne suka tayar da bama-bamai a wasu kauyuka biyu na gundumar Dansadau a karamar hukumar Maru.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara CP Muhammad Shehu Dalijan ne ya bayyana hakan a wata zantawa da manema labarai ta wayar tarho.
CP Muhammad ya tabbatar da tashin bama-baman a kauyen ‘Yar Tasha da ke kan hanyar Dansadau.
- Gwamnatin Kano Ta Mayar Wa Jami’ar Yusuf Maitama Tsohon Sunanta
- Sojojin Isra’ila Sun Saɓa Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Lebanon
Kwamishinan ya ce tashin bama-baman ya yi sanadaiyyar mutuwar mutum daya, yayin da wasu uku suka samu raunuka daban-daban.
An ce bama-baman da ake zargin ‘yan ƙungiyar ta’addar Lakurawa da dasa wa sun tashi da misalin karfe 8 na safiyar ranar Laraba.