Wasu matasa sun kashe wani dan sanda da yake kokarin raba fada tsakanin wasu kungiyoyi da ba sa jituwa da juna a Karamar Hukumar Lavun da ke Jihar Neja.
Dan sandan wanda aka bayyana sunansa da Nasiru, an kashe shi ne a kauyen Manima na unguwar Gaba da ke yankin.
Rahotanni na nuni da cewa, bayan barkewar rikicin, an gayyato jami’an tsaro, inda bayan zuwansu, sai mambobin kungiyoyin suka sare shi da makamai a ka.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa kafin faruwar lamarin, dan sandan ya halarci wani taron zama lafiya a kauyen Doko na Karamar Hukumar ta Lavun, inda aka tattauna batun yawan faruwar rikice-rikice kan filaye a yankin.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar NEJA, DSP Wasiu Abiodun, ya ce tuni suka kama mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin.