• Home  
  • WHO na neman ƙarin kuɗi don daƙile Ebola a Congo
- Babban Labari

WHO na neman ƙarin kuɗi don daƙile Ebola a Congo

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya na neman ƙarin kuɗi don taimaka wa Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo don ta samu ta yaƙi ɓarkewar cutar Ebola. Da yake magana a Kinshasa, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce kashi ɗaya bisa uku na tallafin da ake nema aka samu zuwa yanzu. Amurka ta yi alƙawarin bayar da ƙarin dala miliyan […]

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya na neman ƙarin kuɗi don taimaka wa Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo don ta samu ta yaƙi ɓarkewar cutar Ebola.

Da yake magana a Kinshasa, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce kashi ɗaya bisa uku na tallafin da ake nema aka samu zuwa yanzu.

Amurka ta yi alƙawarin bayar da ƙarin dala miliyan 80 domin tallafa wa ƙoƙarin da ake a Congo da Uganda inda aka tabbatar da wasu mutum bakwai sun kamu da cutar.

WHO ta ce mutum na farko da ya warke daga cutar tuni aka sallame shi daga asibiti.

Cutar ta kashe fiye da mutum 200 inda ake zargin dubbai sun kamu da cutar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000