Home » Yadda Gasar Firimiya ta Najeriya ta Samu ci Gaba ta Fannin Yawan Masu Kallo a Filayen Wasanni.

Yadda Gasar Firimiya ta Najeriya ta Samu ci Gaba ta Fannin Yawan Masu Kallo a Filayen Wasanni.

by Suraj Na iya Kududdufawa
0 comment

Gasar ajin Firimiya ta kasar Najeriya gasa ce wadda aka fara gudanar da ita a shekarar 1972 inda aka baiwa gasar sunaye kala-kala, inda zuwa yanzu ake kiran gasar da suna ajin kwararru.

Kungiyar kwallon kafa ta Mighty Jet na jihar Plateau ne su ka fara kafa tarihin lashe gasar kuma sunan su ya shiga kundin tarihin gasar duk da cewa yanzu basa cikin gasar inda za ace babu kungiyar a yanzu.

Wannan kakar wasan da ake fafatawa ta 2024 zuwa 2025 itace karo ta 54 a tarihi tun daga 1972 zuwa wannan sabuwar shekarar ta 2025.

Daga lokacin zuwa yanzu an samu yawaitar masu kallon gasar musamman a ‘yan shekarunnan inda ake kallon gasar sosai da sosai.

Sai dai har yanzu ana yiwa gasar ajin Firimiya ta Najeriya kallon hadarin kaji musamman yadda cin hanci da rashawa ya mamaye gasar ta ajin kwararru.

Irin wannan matsala da makamantan ta ana ganin sune suke ci gaba da kawowa gasar ta NPFL cikas da rashin ci gaba musamman yadda gasar take samun ci baya a duniya dama Afrika.

Sai dai a yanzu ana ganin an dan samu sauyi ta wasu fannonin ganin yadda akeson aga an samu sauye sauye wajen inganta gasar, inda daga ahekaru 2 zuwa yanzu an samu sauye sauye sosai.

Amma kuma an yabawa gasar musamman yadda ake samun magoya bayan kwllon kafa suke cika filayen wasa da zarar kungiyar da suke goyon baya tana fafata wasa a gida.

Haka zalika idan ana fafata wasannin hamayya na yanki daya akan hango filin wasa yayi cikar kwari, misali idan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da Katsina United suna fafata wasa filin yakan cika inda akan kira wasan da suna wasan hamayya na arewa maso yamma.

Bugu da kari idan manyan kungiyoyin kwallon kafa suna fafatawa a tsakaninsu akan hango filin wasan yayi cikar kwari, misali idan ana wasa tsakanin Rivers United da Enyimba ko Kano Pillars da Enyimba ko Enugu Rangers da Enyimba ko da sauransu.

Ita kanta gasar kungiyar kwallon kafa ta Enyimba tafi yawan lashe gasar inda take da kofin har guda 9, sai Enugu Rangers na da guda 8 sai Iwanyanyu National 5 yayin da Kano Pillars take da gasar guda 4.

A yanzu dai gasar ajin NPFL ta Najeriya ta kasance tana kara samun yawan magoya baya a filayen wasanni daban-daban sakamakon gyara da akeyi a gasar sabanin shekarun baya.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?