Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya amsa gayyatar da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC tayi masa.
A cewar mai Magana da yawun tsohon gwamnan, wanda ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba, “tsohon gwamnan ya yanke hukuncin ne bayan shawara da iyalansa da lauyoyinsa da sauran abokan siyaysa.” A cewar hadimin na sa.
A watan Aprilu da ya gabata ne Hukumar ta EFCC ta fara farautar Yahaya Bello ruwa a jallo, sai dai bayan ƙawanya da jami’an hukumar sukayi a gidan sa , Gwamanan Jihar mai ci Usman Ododo ya shiga da jami’an tsaro kuma ya hana tafiya da tsohon gwamnan.
Ana zargin Yahaya Bello ne dai da wawure tsabar kuɗi da suka tasarma Naira Miliyan Dubu takwas da Miliyan ɗari biyu da arba’in da shida a lokacin da yake gwamnan jihar.