A daren yau Talata 17 ga Satumba za’a fara gasar cin kofin zakaru ta Nahiyar Turai na kakar wasan 2024/2025.
Cikin wani salo da ba’a taɓa ganin irinsa ba, ƙungiyoyi guda 36 ne zasu fafata, saɓanin a baya da aka saba ganin guda 32.
Inda duk rukuni zai sami ƙungiyoyi guda takwas. kowace ƙungiya dai zata fafata wasanni guda huɗu a gida, hudu a waje.
Real Madrid ce dai ta lashe gasar a kakar wasan da ta gabata.
#championsleague #UEFA#muhasa