• Home  
  • Yan Sanda Sun Kama Ɓarayin Wayar Lantarki A Katsina
- Labarai

Yan Sanda Sun Kama Ɓarayin Wayar Lantarki A Katsina

Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina ta kama wasu mutane uku da ake zargi da sata tare da lalata kayan gwamnati. Jami’an da ke aiki a rundunar da ke Rimi da suke kan sintirin yau da kullum a ƙaramar hukumar, tare da haɗin gwiwar al’ummar gari ne suka yi nasarar cafke waɗannan mutane uku ɗauke da […]

Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina ta kama wasu mutane uku da ake zargi da sata tare da lalata kayan gwamnati.

Jami’an da ke aiki a rundunar da ke Rimi da suke kan sintirin yau da kullum a ƙaramar hukumar, tare da haɗin gwiwar al’ummar gari ne suka yi nasarar cafke waɗannan mutane uku ɗauke da kebul na wutar lantarki da ake zargin na sata ne.

Jami’an da ke aiki a rundunar da ke Rimi da suke kan sintirin yau da kullum a ƙaramar hukumar, tare da haɗin gwiwar al’ummar gari ne suka yi nasarar cafke waɗannan mutane uku ɗauke da kebul na wutar lantarki da ake zargin na sata ne.

Waɗanda aka kama su sun haɗa da: Mansur Suleiman, mai shekara 23 da Mansur Hamza, mai shekara 21 da Jibrin Ahmed, mai shekara 28. Sun yi nasarar kama su ne a ranar 2 ga watan Agusta, 2026 da misalin ƙarfe 8:30 na dare.

A yayin binciken farko da aka gudanar, an gano waɗannan abubuwa a hannunsu da suka haɗa da: Mita 60 na kebul na wutar lantarki mai kaurin 100mm da ake zargin an sace, zarto guda ɗaya, almakashi guda ɗaya, wuƙa guda ɗaya, laya babur guda ɗaya da ganye busasshe da ake zargin wiwi ne.

Yanzu haka waɗanda ake zargin suna tsare a hannun ’yan sanda kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike, kamar yadda sanarwar da ta fito daga Kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiƙ Aliyu.

Sanarwar ta ƙara da cewa, Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Ali Umar Fage ya yaba wa al’umma bisa sa ido da haɗin kai da suke bai wa ’yan sanda wajen yaƙi da masu lalata kayan jama’a.

Ya kuma yi gargaɗi ga duk masu hannu a sata da lalata dukiyar gwamnati ko ta ƙashin kai da su daina, yana mai jaddada cewa duk wanda aka kama yana aikata irin wannan laifi zai fuskanci hukunci mai tsanani kamar yadda doka ta tanada.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai