Rundunar ’yan sanda ta kama wani matashi ɗan shekara 29, mai suna Abubakar Isah Mokwa ɗalibi da yake karatun digiri na biyu a tsangayar Tattalin Arziki na Noma a Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida, Lapai, Jihar Neja, An kama ɗalibin ne bisa zarginsa da sukar Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago.
Rahotanni sun ce an an kama Abubakar Mokwa ne a wajen harabar jami’ar da yake da masauki a Lapai a ranar Alhamis bayan wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya caccaki gwamnan kan rashin aikin yi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ne ya tabbatar wa Aminiya kamun da aka yi wa ɗalibin.
Ya ce, an kama wanda ake zargin ne biyo bayan ƙorafin da ya yi kan cin zarafi ta intanet, satar bayanai ta intanet da sauran laifukan da suka shafi intanet.
- Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Dan Uwansa A Matsayin Sabon Sarkin Duguri
- Shugaba Tinubu Ya Sauya Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya
“Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta samu ƙorafin aikata laifukan da suka haɗa da cin zarafi ta intanet, satar bayanai ta intanet da sauran laifukan da suka shafi intanet akan wani Abubakar Isah Mokwa mai shekara 29 a garin Mokwa kuma ɗalibin IBBUL da yake karatun digiri na biyu.
“Saboda haka, hukumar jami’an Lapai ta gayyace shi ta kama shi a ranar 23 ga Oktoba, 2025 da misalin ƙarfe 11 na dare, sannan aka tura shi hedikwatar ‘yan sanda ta jihar a Minna babban birnin jihar, domin ci gaba da bincike kan ƙarar da ake tuhumarsa da aikatawa. Sai dai wanda ake zargin yana tsare kuma za a ci gaba da yi wa jama’a ƙarin bayanui,” in ji Abiodun.

