Wani matashin ɗan kasuwa mai suna Isma’il Makaye ya rasu a wani yanayi da har yanzu ba a bayyana ba a gidan budurwarsa, wata fitacciyar mai yin bidiyon TikTok a Kano da aka fi sani da Fati Cele, da ke unguwar Danbare a ƙaramar hukumar Kumbotso ta jihar Kano kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Rahotanni sun ce marigayin, wanda ke sana’ar kayan kwalliya a yankin Hotoro Tishama, ya mutu ne da sanyin safiyar Juma’a, lamarin da ya sa jami’an ‘yansanda suka fara bincike kan musabbabin mutuwarsa.
Wani abokin marigayin, Hassan Mohammed, ya ce lokacin da suka isa gidan tare da jami’an ‘yansanda sun tarar da Isma’il ya riga ya rasu. Ya ce an fara kai gawarsa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad kafin daga bisani a mayar da ita Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase, inda aka tabbatar da rasuwarsa.
Hassan ya bayyana cewa Isma’il da Fati Cele sun shafe sama da shekara biyu suna soyayya, sai dai sun rabu na wani lokaci bayan marigayin ya yi aure, kafin daga baya su koma tare.
Ya kuma ce an samu wayoyin marigayin da makullan motarsa a wurin da lamarin ya faru. A cewarsa, an ga raunuka a kansa tare da alamun jini, lamarin da ya sa suke zargin cewa an buge shi da wani abu.
An yi jana’izar marigayin a ranar Juma’a a Unguwa Uku Yan Awaki bisa koyarwar addinin Musulunci.
Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, musamman a TikTok, inda masu amfani da dandalin suka bukaci a gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar.

