Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce kusan kananan yara dubu dari biyu da hamsin (250,000) a Kano ba su taba samun allurar riga-kafi na yau da kullum ba, lamarin da ya sa Kano ta kasance jiha mafi yawan wadan da ba a musu riga kafi a Najeriya.
Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahma Rihood Mohammed ne ya bayyana hakan yayin wani taron karawa juna sani na shugabanni da hakimai a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.
A cewarsa, adadin masu kamuwa da cutar shan inna a Kano ya karu daga kashi 6 a shekarar 2022 zuwa kaso 27 a shekarar 2023 da kuma kashi 29 a shekarar 2024.
Rahma Rihood ya bayyana allurar rigakafi a matsayin hanya mafi inganci don kare yara daga cututtuka irin su polio, kyanda, da kuma Mashako,
Ya ce idan suka samu goyon bayan gwamnati, shugabannin kananan hukumomi, da cibiyoyin gargajiya, Kano za ta iya shawo kan wadannan kalubale da gina al’umma mai koshin lafiya.
A nasa jawabin, kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Labaran Yusuf, ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na inganta harkokin kiwon lafiya a jihar.
Ya ce gwamnati mai ci ta karkata akalar samar da kiwon lafiya idan aka kwatanta da yadda ta cimma da kuma ta himmatu wajen samar da alluran rigakafi, kawar da cutar shan inna da kuma haddasa mutuwar mata masu juna biyu jim kadan a jihar.
Babban daraktan hukumar kula da lafiya matakin farko na jihar Kano, Dokta Nasir Mohammad Mahmud ya bayyana cewa taron bitar na da nufin sabunta masu ruwa da tsaki kan alkaluman kiwon lafiya, rigakafi, kawar da cutar shan inna da kuma alluran rigakafin da ba a taba samu a jihar ba.
“Yadda za a shawo kan lamarin, sanar da su ayyuka daban-daban da nauyin da ya rataya a wuyansu kan hakan da kuma tabbatar da sadaukarwarsu”
Taron wanda aka yi wa lakabi da taron tattaunawa da shugabannin kananan hukumomi domin ci gaba da samun nasarorin da aka samu na cutar shan inna, rigakafin rigakafi da sauran ayyukan PHC a jihar Kano wanda hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar Kano KSPHCMB tare da hadin gwiwar UNICEF suka shirya.