Home » NHIS Ta Bullo Da Shirin Raba Daidai Wurin Siyan Maganin Kansa A Najeriya

NHIS Ta Bullo Da Shirin Raba Daidai Wurin Siyan Maganin Kansa A Najeriya

Mista Ohiri ya ce wannan wani mataki ne na rage tsadar kiwon lafiya ta amfani da hasken radiyeshin wadda na cikin muhimman hanyoyi na magance cutar a yayind a duniya ke tuna wa da ranar masu fama da cutar kansa a duniya. Domin magance tsadar wannan hanya ta kiwon lafiya, hukumar NHIA tana ba da tallafin kaso 50% na kudin maganin da za a biya wanda ya kai Naira 400,000.”

by Zubaidah Abubakar Ahmad
0 comment

Hukumar kula da inshoran lafiya ta ƙasa (NHIs), ta ɓullo da wani shiri na raba daidai wurin sayen magani ga masu fama da cutar kansa a Najeriya.

A ƙarƙashin shirin, waɗanda suke fama da cutar kansa kuma suke samun kulawar kikitoci za su samu tallafin da ya kai Naira 400,000 domin inganta lafiyarsu.

Darakta-janar na hukumar, Kelechi Ohiri, ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na ƙasa, (NAN) a Abuja.

Mista Ohiri ya ce wannan wani mataki ne na rage tsadar kiwon lafiya ta amfani da hasken radiyeshin wadda na cikin muhimman hanyoyi na magance cutar a yayind a duniya ke tuna wa da ranar masu fama da cutar kansa a duniya.

“Domin magance tsadar wannan hanya ta kiwon lafiya, hukumar NHIA tana ba da tallafin kaso 50% na kudin maganin da za a biya wanda ya kai Naira 400,000.”

Sannan ya ce hukumar tana haɗin guiwa da cibiyoyin lafiya da ke kula da masu fama da cutar ƙari a faɗin Najeriya domin cimma burin inganta tsarin maganin kula da masu kansa.

“Sannan hukumar na ƙoƙarin ganin ta ƙara yawan cibiyoyin ba da maganin kansa da ta tantance da ƙarfafa alaƙarta da sauran kamfanonin magunguna da masu samar da kayan aiki domin tabbatar an zamantar da wadatar da Najeriya da fasahar da ake da buƙata.”

Sannan ba ya ga amfani da hanyar neman lafiya ta “radiotherapy’ (amfani da hasken radiyeshin wajen magance cuta) zuwa ga bunƙasa tsarin neman lafiya na “oncology” (magance cutar ƙari).

Ya ce ta hanyar shirin Inshora na ɗaiɗaikun mutane da na iyali (GIFSHIP), hukumar NHIA na ba da damar samun kulawa ga masu cutar kansa.

Darakta-janar ɗin ya ce hukumar na kula haɗa kai da manyan kamfanonin magani kamar Roche da Pfizer domin kawo magunguna da za ta ɗauki nauyin rabin kuɗinsu, inda marasa lafiya za su biya rabin.

Ya ce tuni kusan mutane 200 suka fara amfani da shirin kula da lafiyar a manyan cibiyoyi a Najeriya.

Shi ma shugaban kwararru a fannin cutar kansa ta Najeriya, Adamu Umar, ya jinjina wa hukumar kan ɓullo da wannan shiri yana mai bayyana ta a matsayin babban mataki na samar da cigaba.

Ya bayyana muhimmancin amfani da hasken radiyeshin ga masu fama da cutar a babban mataki da kuma bayyana tsarin raba daidai na kuɗin magani da cewa zai taimaka wajen rage wahalar da marasa lafiya ke shada iyalansu.

“Shirin NHIA yana kan hanya kuma marasa lafiya da yawa za su amfana da shirin…” ya faɗa.

Gwamnati za ta gina gidaje sama da 10,000 wa ma’aikatan asibitocin kasar nan

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?