Tsaro/ Rundunar ‘Yan Sanda
Ya yin da ya rage kasa da mako daya a gudanar da zaben gwamnoni da na yan’majalisar dokokin jihohi a kasar nan, Jami’an tsaro sun ce, sun gano wasu shirye-shiryen da manyan jam’iyyu masu adawa da juna ke yi domin tayar da fitina a lokacin zaben a wasu Jihohi.
Wannan na zuwa ne lokacin da gamayyar rundunar jami’an tsaro a Sakkwato ta ce ta kama makamai a hannun wasu magoya bayan wata jam’iyya kuma tana sane da shirin da wata jam’iyya ke yi na daukar fansa akan zargin da take yi.
Gamayyar rundunar jami’an tsaro a jihar ta Sokoto, ta ce, ta sami wasu bayanan tsaro na sirri na yunkurin jan daga tsakanin manyan jam’iyun jihar na APC da PDP masu hamayya da juna.
Jam’iyyun na APC da PDP na kokarin ramuwar gayya ne bisa zargin da suke wa junansu na hana zaɓe a wasu runfunan zaɓe sama da 300 a lokacin zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalissa a ranar 25 ga watan Fabarairun da ya gabata.
Shugaban gamayyar jami’an tsaron kuma kwamishinan ‘ƴan sandan Jihar ta Sokoto Muhammad Hussaini Gumel nuna buƙatar a kata wa wannan yinƙuri birki, gabanin zuwan zaɓen da kuma bayan zaɓen gwamnonin da ake tunkara a ranar 11 ga wannan watan da muke ciki.