• Home  
  • Ƙungiyoyin PDP 293 sun koma APC a Yobe
- Babban Labari - Siyasa

Ƙungiyoyin PDP 293 sun koma APC a Yobe

A wani gagarumin sauyin siyasa a Jihar Yobe, ƙungiyoyi 293 na Jam’iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa APC a Ƙaramar Hukumar Potiskum.   Sauyin sheƙar wanda shi ne mafi girma a yankin a ’yan kwanakin nan ya samu jagorancin Shugaban PDP na Ƙaramar Hukumar Potiskum, Alhaji Audu Hamisu, wanda aka fi sani da Soja Boy. Masu […]

A wani gagarumin sauyin siyasa a Jihar Yobe, ƙungiyoyi 293 na Jam’iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa APC a Ƙaramar Hukumar Potiskum.  

Sauyin sheƙar wanda shi ne mafi girma a yankin a ’yan kwanakin nan ya samu jagorancin Shugaban PDP na Ƙaramar Hukumar Potiskum, Alhaji Audu Hamisu, wanda aka fi sani da Soja Boy.

Masu sauya sheƙar sun fito ne daga manyan unguwanni da dama a Potiskum, ciki har da Tora-Bora, Texaco, Sokol-Jigawa, Dorawa, Kabul, Kamfala, Old Kwata, Rasha da Big Soja.

Da yake jawabi a wajen taron maraba da sabbin mambobin, Shugaban APC na Jihar Yobe, Alhaji Muhammad Gadaka, ya bayyana jam’iyyar a matsayin mai haɗaka da maraba da kowa, yana mai danganta ƙarfinta da yawan masu shigowa cikinta a kullum.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai