Zauren haɗin kan malamai da ƙungiyoyin musulinci a faɗin jihar Kano, sun bayyana kaɗuwarsu kan yadda wani taron siyasa ya janyo zubar da jini da kuma rasa rayukan jama’a.
Sakataren zauren haɗin kan malaman, Dr. Sa’id Ahmad Dukawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba manema labarai.
Haɗakar ƙungiyoyin sun yi kira musamman ga ƴn siyasa da suke haddasa faɗan daba,su sani cewar Manzon Allah, Sallallahu-Alaihi wassalam, ya ce idan mutanen suka yi faɗan gaba kuma yakai ga kisa, makomar mai kisan da kuma wanda aka kashe wuta ce, domin shi ma wanda aka kashen da ya samu dama kisan zai yi.
Haka zalika zauren yayi Ala-wadarai da miyagun maganganu da zage-zage da wasu ƴan siyasa suke yi a jihar Kano, tare da yaba wa gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya tsawatarwa da wasu mata da suka nuna wata mummunar ɗabi’a ƴan kwanakinnan, inda suka yi fatan zai yi makamanciyar tsawatarwar ga waɗanda suka yi faɗan daba da masu saka su dama waɗanda suke yin wani abu na rashin tarbiyya don kar su janyowa al’ummar Annabi fushin Ubangiji.
A ƙarshe ƙungiyar ta yi addu’ar Allah ya ci gaba da zaunar da jihar Kano lafiya.
