A wani gagarumin sauyin siyasa a Jihar Yobe, ƙungiyoyi 293 na Jam’iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa APC a Ƙaramar Hukumar Potiskum.
Sauyin sheƙar wanda shi ne mafi girma a yankin a ’yan kwanakin nan ya samu jagorancin Shugaban PDP na Ƙaramar Hukumar Potiskum, Alhaji Audu Hamisu, wanda aka fi sani da Soja Boy.
Masu sauya sheƙar sun fito ne daga manyan unguwanni da dama a Potiskum, ciki har da Tora-Bora, Texaco, Sokol-Jigawa, Dorawa, Kabul, Kamfala, Old Kwata, Rasha da Big Soja.
Da yake jawabi a wajen taron maraba da sabbin mambobin, Shugaban APC na Jihar Yobe, Alhaji Muhammad Gadaka, ya bayyana jam’iyyar a matsayin mai haɗaka da maraba da kowa, yana mai danganta ƙarfinta da yawan masu shigowa cikinta a kullum.
Ya yaba wa manufofin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da na Gwamna Mai Mala Buni, tare da kira ga sabbin mambobin da su bayar da gudummawa wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓe mai zuwa.
“Jam’iyyar APC dandali ce mai faɗi da ke ba da dama iri ɗaya ga dukkan ‘yan jam’iyya, ba tare da la’akari da asalinsu ba. Don haka ina roƙonku da ku haɗa kai cikin sauri ku yi aiki don nasarar jam’iyyar a zaɓe mai zuwa,” in ji Gadaka.
A nasa jawabin, Hamisu ya ce shawarar ficewa daga PDP ta biyo bayan shawarwari da sake nazarin ayyukan APC a matakin jiha da tarayya.
Ya bayyana ci gaban tsaro, manufofin tattalin arziki da ci gaban jama’a a matsayin muhimman dalilan da suka sa su sauya sheka.
“Bayan yin nazari mai zurfi, mun gamsu cewa makomar siyasarmu tana hannun APC,” in ji shi.
