• Home  
  • Ƴan bindiga sun yi garkuwa da dattijan da suka je neman sulhu a Zamfara
- Babban Labari

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da dattijan da suka je neman sulhu a Zamfara

Ƴan bindiga sun riƙe dattijan wani ƙauye a ƙaramar hukumar Maradun da ke jihar Zamfara bayan sun yi yunƙurin yin sulhu sanadiyyar rashin tsaron da ke addabar yankin. Lamarin ya faru ne a ƙauyen mai suna Magamin Diddi wanda rahotanni suka ce yana a kusa da ɗaya daga cikin dazukan da ƴan fashin daji ke […]

Ƴan bindiga sun riƙe dattijan wani ƙauye a ƙaramar hukumar Maradun da ke jihar Zamfara bayan sun yi yunƙurin yin sulhu sanadiyyar rashin tsaron da ke addabar yankin.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen mai suna Magamin Diddi wanda rahotanni suka ce yana a kusa da ɗaya daga cikin dazukan da ƴan fashin daji ke da sansani.

A tattaunawarsa da BBC, shugaban ƙaramar hukumar Maradun Sunusi Ahmed Dosara ya ce: “Tun wata uku da suka wuce (ɓarayi) sun hana su (ƙauyen) zaman lafiya, ana cikin haka ne sai ɓarayin suka kwaɗaita musu cewa su zo a yi sulhu domin su bar su, su riƙa cin kasuwa.

“To daga nan sai dattijai suka je daji domin haɗuwa da ƴan bindiga, amma a lokacin da suka je sai ɓarayin suka riƙe su, sanan suka sako wasu daga cikinsu suka ce ba za su sake su ba sai an cika musu wasu sharuɗaɗa”.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce daga ƙididdigar da suka yi mutanen da ƴan fashin dajin suka riƙe “sun kai 39”.

Ya ƙara da cewa dukkanin mutanen da ake riƙe da su “maza ne dattawa”.

“Yanki ne wanda wadannan ɓarayi sun daɗe suna cin karensu babu babbaka,” a cewar shugaban ƙaramar hukumar ta Maradun.

Ya ce dajin wanda ake kira Bayan Ruwa, daga cikin shi ne ɓarayi ke fitowa suna tare matafiya da ke kan hanya daga Zamfara zuwa Sokoto da kuma Koko, inda suke yin garkuwa da mutane.

“Wannan daji shi ne maɓoyarsu, duk wani ɓarawo da aka koro, idan ya shiga wannan daji tamkar ya tsira ne.”

Zamfara na cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da suka daɗe suna fama da matsalar ƴanfashin daji masu kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Ayyukan ƴan bindigar sun durƙusar da harkokin tattalin arziƙi a yankin, musamman noma, wanda akasarin al’ummar yankin ke dogaro da shi

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai