Sojojin Najeriya sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane tare da ceto mutum 23
Sojojin Najeriya sun ce sun ceto mutane 23 da aka yi garkuwa da su, tare da daƙile wani yunƙurin sace wasu mutane a yayin samamen da suka kai kan ƴanbiniga a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda jaridar Daily Post mai zaman kanta ta ruwaito a ranar 5 ga watan Satumba. […]









