Kasar Burtaniya ta sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da bai kamata a rika ɗaukar ma’aikatan kiwon lafiya da walwalar jama’a aiki ba.
Hukumar lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar wani rahoto inda ta ce Najeriya na buƙatar tallafi a ɓangaren kula da lafiya.
Idan za a iya tunawa Muhasa Radio ta haɗa wani rahoto a watan Maris, inda hukumar ta WHO ta buga jerin sunayen ƙasashe masu bukatar agaji a fannin lafiya waɗanda suka ƙunshi ƙasashe 55, ciki har da Najeriya da ke fama da karancin ma’aikatan lafiya.
Gwamnatin Burtaniya ta ce ya kamata a bai wa Najeriya da sauran ƙasashen da ke cikin wancan jerin sunaye fifiko don bunƙasa harkokin lafiya wanda zai ba wa ma’aikatan lafiya da ke fitowa daga ƙasar damar samun guraben aiki ƙasashen duniya.