Gwamnatin Yobe ta ware Naira miliyan 103 domin ciyar da marasa galihu da kuma kula da malamai masu wa’azi a lokacin azumin watan Ramadan na bana a jihar.
Da yake zantawa da manema labarai a garin Damaturu na jihar Yobe, Kwamishinan Harkokin Addini, Alhaji Mala Musty, ya ce Gwamna Buni ya amince da kashe Naira miliyan 73 wajen sayen raguna da kayan dafa abinci a cibiyoyin ciyar da abinci 67 da aka samar a jihar tun farkon azumin zuwa yanzu har zuwa ƙarshensa.
An kuma ware Naira miliyan 30 domin biyan alawus ga malamai masu wa’azi a lokacin azumin na bana.
Kwamishinan addini, ya ce sun shirya sanya jami’ansu su zagayawa domin duba duk wuraren da ake ciyar da abincin, don ba za su iya barin mutane su je su yi duk abin da suka ga dama ba.
Ya ce tun kafin zuwan Gwamna Buni al’adar gwamnatin Jihar Yobe ce ciyar da mabukata a watan Ramadan da sunan “Iftar”.
Kwamishinan addini ya bayyana cewa gwamnati ta ware buhunhunan shinkafa 1,050 domin ciyarwa har zuwa karshen watan Ramadan.