Hukumar kula da aikin Haji da Umrah ta Saudiyya ta yi kira ga masu ziyarar ibada da su guji ɗauke-ɗauken hotuna a yayin gudanar da ibada a wurare masu alfarma.
Hukumar ta ce bai kamata masu ziyarar ibadar su ɓige da ɗaukar hotuna ba a maimakon mayar da hankali kan ibadar da ta kai su ƙasar.
Haka kuma hukumar ta gargaɗi masu ɗaukar hotunan da su guji ɗaukar hoton da fuskokin mutane a cikin hoton nasu ba tare da izini ba.
Sannan ta bayyana cewar masu ziyarar ibadar su daina tsayawa don ɗaukar hoto a wuraren da jama’a da dama ke taruwa, domin a cewarta hakan na janyo cunkuson jama’a a wuraren.
A baya-bayan nan dai mutane sun ɓullo da salon ɗaukar hotuna a lokacin ziyarar Umrah ko Aikin Hajji tare da wallafawa a shafukansu na sada zumunta.
Lamarin da wasu malamai ke ganin cewa yawan yin hakan ka iya zama ‘Riya’, abin da kuma a cewar malaman zai iya ɓata wa mutane niyyar ibadar tasu.