• Home  
  • Ƴan sandan Kano sun ƙwato motocin sata 3 tare da kama mutane uku da ake zargi
- Babban Labari

Ƴan sandan Kano sun ƙwato motocin sata 3 tare da kama mutane uku da ake zargi

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama mutane uku da ake zargi da satar motocin jama’a, tare da ƙwato motoci uku da ake zargin na sata ne. Waɗanda aka kama sun haɗa da Abel Nanlir Nafa daga Abuja, Stephen Wanneh daga jihar Kaduna, da Habiba Mohammad daga Kano. Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, CSP […]

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama mutane uku da ake zargi da satar motocin jama’a, tare da ƙwato motoci uku da ake zargin na sata ne.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Abel Nanlir Nafa daga Abuja, Stephen Wanneh daga jihar Kaduna, da Habiba Mohammad daga Kano.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa, sun kama waɗanda ake zargin kan wata mota ƙirar Toyota Camry, da aka sato daga jihar Enugu, sannan suka sake ƙwato wasu motocin biyu a jihar Kano.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano , CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce rundunar za ta ci gaba da yaƙi da masu aikata laifuka da kuma ci gaba da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000