50
Ƙungiyar da ke tallafa wa marasa galihu ta SURE4YOU ta taimaka wa mata 30 iyayen marayu da kayan abinci da sutura da kuma kuɗaɗe a jihar Katsina. Ƙungiyar da ke karkashin jagorancin wanda ya assasa ta, tsohon shugaban hukumar shigi da fici ta ƙasa, Muhammad Babandede, ta bayar da tallafin ne a ranar Laraba 14 ga watan Agusta.
Wakilinmu Ismail Sulaiman Sani ya ruwaito mana cewa, shugaban gudanarwar ƙungiyar, tsohon kwanturolan hukumar shigi da fici ta ƙasa, Mannir Yari, ya bayyana manufar taron inda yace an raba wa matan 30 da mazajensu suka rasu, kayan abinci da suka haɗa da buhun shinkafa da sukari da man gyada da kuɗi Naira dubu biyar-biyar kuma dukansu suka samu turmin atamfa ɗaya-ɗaya. Ya kuma ƙara da cewa wannan matakin farko ne na tallafin, inda yace kungiyar za ta sake komawa gidajensu don duba halin da suke ciki.
Mannir Yari yayi kira ga al’umma su riƙa kawo gudunmowa domin taimakawa ayyukan ƙungiyar. A jawabinta, sakatariyar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Katsina, Hajiya Binta Ɗangani, ta yi kira ga iyayen marayun su yi kyakkyawan amfani da tallafin da aka ba su.
A baya dai ƙungiyar ta SURE4YOU ta gudanar da irin wannan taron tallafa wa mata iyayen marayu a jihohin Kano, da Jigawa, da kuma Abuja babban birnin tarayya.