Home » Ƙungiyar Miyatti Allah Ta Zargi Wasu ‘Yan sa-kai da Kashe Mata Mambobi 12

Ƙungiyar Miyatti Allah Ta Zargi Wasu ‘Yan sa-kai da Kashe Mata Mambobi 12

by Anas Dansalma
0 comment

Kungiyar Fulani Makiyaya Miyetta Allah, ta yi shelar cewar ‘Yan sa-kai a Jihar Sakkwato sun halaka mambobinta 12 sakamakon wani farmakin da suka kai matsugunansu da ke yankin Gwadabawa.

Shugaban kungiyar ta kasa, Baba Usman Ngelzerma ya ce wannan rikici ya barke ne tun a ranar juma’a sakamakon harin da tawagar ‘Yan sa-kan suka kai matsugunan makiyayan, abin da ya kai ga rasa rayuka da kuma kona rugagen Fulanin.

Ngelzerma ya ce daga cikin matsugunan Fulanin da aka kai wa hari sun hada da Tsola da Asara da Karan biki da kuma Sakamaro duka a yankin Gwadabawa, kuma an jikkata mutane da dama.

Lokaci zuwa lokaci ana samun arangama tsakanin Fulani makiyayan da ‘Yan sa-kai abin da ke kai ga rasa rayuka, a inda  Shugaban kungiyar Fulanin na kasa, Baba Usman Ngelzerma ya bukaci gwamnati da ta tashi tsaye wajen dakile wannan matsala da kuma hukunta duk wadanda aka samu suna da hannu a ciki.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi