Gwamnan Kano Ya Yaba wa CP Ibrahim Bakori Kan Ceto Shugaban APC Na Rogo a Hannun Masu Garkuwa
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa rundunar ’yan sandan jihar bisa nasarar ceto shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Rogo, Abdullahi Alasan Beli, wanda aka fi sani da Abdullahi Fanka, bayan shafe kwanaki 68 a hannun masu garkuwa da mutane.
An yi garkuwa da shugaban jam’iyyar ne a gidansa da ke garin Beli, a ƙaramar hukumar Rogo, inda masu garkuwar suka riƙa sauya masa wuraren da suke tsare dashi zuwa Danja, Ikara da Giwa a jihar Kaduna, da kuma wasu sassan jihar Zamfara.
Kwamishinan ’yan sandan Kano, CP Adamu Bakori, ne ya bayyana nasarar ceton nasa yayin ganawarsa da gwamnan a gidan gwamnati da ke Kano, inda ya ce an gudanar da aikin ne ta hanyar amfani da dabarun tsaro.
Gwamna Yusuf ya yaba wa kwamishinan ’yan sandan da jami’an rundunar, musamman waɗanda suka taka rawa wajen aikin, ciki har da CSP Aliyu Muhammad Auwal da CSP Ado Muhammad Audi.
Haka kuma, gwamnan ya umarci kwamishinan lafiya na jihar da ya tabbatar an ba wanda aka ceto cikakkiyar kulawar lafiya da duk abunda ya shafi lafiyarsa.
Gwamnan ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
