• Home  
  • Ƙungiyar MURIC ta buƙaci hukumar DSS ta gaggauta sakin Walida.
- Babban Labari - Labarai

Ƙungiyar MURIC ta buƙaci hukumar DSS ta gaggauta sakin Walida.

Ƙungiyar MURIC ta buƙaci hukumar DSS ta gaggauta sakin Walida. Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi a Nageriya (MURIC) ta buƙaci Babban Daraktan DSS da ya bi umarnin kotu ya saki Walida Abdulhadi, da ke hannun hukumar a Abuja. ‎ ‎MURIC ta ce kotu ta bayar da umarnin a mayar da ita garinsu, Hadejia jihar Jigawa a […]

Ƙungiyar MURIC ta buƙaci hukumar DSS ta gaggauta sakin Walida.
Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi a Nageriya (MURIC) ta buƙaci Babban Daraktan DSS da ya bi umarnin kotu ya saki Walida Abdulhadi, da ke hannun hukumar a Abuja.
‎MURIC ta ce kotu ta bayar da umarnin a mayar da ita garinsu, Hadejia jihar Jigawa a ranar 7 ga Janairu, 2026, haka kuma ta nemi ‘yan sanda su gurfanar da wanda ake zargi da sace ta, Ifeanyi Onyewuenyi.
‎Shugaban MURIC na Kano, Malam Hassan Sani Indabawa, ya nuna damuwa kan rashin aiwatar da umarnin duk da gyare-gyaren da ake cewa ana yi a DSS ƙarƙashin jagorancin Mista Oluwatosin Ajayi, ya ce abin damuwa ne yadda zargin sacewa da wasu manyan laifuka ke ci gaba da zama a duƙunƙune.
‎A ɗaya ɓangaren Gwamnatin Jigawa, ta tabbatar da cewa tana bibiyar lamarin, inda aka bayyana cewa Gwamna Umar Namadi ya fara tuntubar manyan jami’ai domin tabbatar da adalci, tare da roƙon jama’a su kwantar da hankalinsu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai