• Home  
  • Ƴan bindiga sun sace tsohon mai magana da yawun soji a Katsina
- Babban Labari

Ƴan bindiga sun sace tsohon mai magana da yawun soji a Katsina

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Najeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, tare da matarsa a Jihar Katsina. Wani rahoto da jaridar Daily Post ta wallafa ya nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar a yankin Matazu yayin da tsohon […]

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Najeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, tare da matarsa a Jihar Katsina.

Wani rahoto da jaridar Daily Post ta wallafa ya nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar a yankin Matazu yayin da tsohon jami’in sojan da matarsa ke tafiya zuwa birnin Katsina.

Maharan sun tare motarsu tare da tafiya da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Wata majiya ta tsaro ta bayyana cewa direban motar ya samu raunin harbin bindiga lokacin harin, amma ya yi nasarar tserewa.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina da kuma rundunar sojoji ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000