• Home  
  • Ɗan sanda ya rasa ransa a artabu da ɓarayin shanu a Katsina
- Babban Labari - Labarai

Ɗan sanda ya rasa ransa a artabu da ɓarayin shanu a Katsina

Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, ɗauke da muggan makamai sun kai hari a ƙauyen Magaje, cikin ƙaramar hukumar Rimi ta Jihar Katsina kuma sun saci dabbobi da dama suka tsere daga garin kafin isowar ’yan sanda. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a 13 ga Fabrairu, 2026 da misalin ƙarfe 02:00 […]

Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, ɗauke da muggan makamai sun kai hari a ƙauyen Magaje, cikin ƙaramar hukumar Rimi ta Jihar Katsina kuma sun saci dabbobi da dama suka tsere daga garin kafin isowar ’yan sanda.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a 13 ga Fabrairu, 2026 da misalin ƙarfe 02:00 na tsakar dare

Da samun rahoton lamarin ba tare da jinkiri ba, Baturen’ Yansandan Rimi (DPO) tare da haɗin gwiwar sassan da ke maƙwabtaka da su da Sojoji, suka tattara jami’ai suka mayar da martani ga maharan.

Tawagar jami’an tsaron ta yi nasarar gano dabbobin tare da kamo wasu daga cikin waɗanda ake zargi da kai wannan hari da makami a ƙauyen Magaje, bayan yin musayar wuta tsakanin jami’an tsaron da su maharan.

Anyi nasarar dawo da dukkan dabbobin da aka sace tare da kashe ‘yan fashin mutum uku.

Daga bisani, ‘yan fashin sun harbi shi DPOn da bindiga wanda ya yi sanadiyar rasa ransa, sai kuma wani ɗan sandan da ya ji rauni a hannunsa, kamar yadda Kakakin rundunar DSP Abubakar Sadiƙ Aliyu ya sanar.

An kai jami’in da ya ji rauni zuwa asibiti mafi kusa don neman kulawar likita kuma yana amsar magani.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar ta Katsina, CP Bello Shehu,  yayin da yake yaba wa aikin jarumtaka da abokantakar sauran tawagar tsaro ta haɗin gwiwar ta nuna, a ɗaya gefen ta yi Allah wadai da wannan mummunan lamari.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai