• Home  
  • DSS ta kama wanda ya sace yaro dan shekara 5 a Kano
- Babban Labari - Labarai

DSS ta kama wanda ya sace yaro dan shekara 5 a Kano

Hukumar  tsaron ta farin kaya (DSS) ta samu nasarar ceto wani yaro mai shekaru biyar, mai suna Muhammad Haruna, daga hannun masu garkuwa da mutane a Kauyen Danzaki, karamar hukumar Gezawa. An gudanar da aikin ceton ne da misalin ƙarfe 7:40 na yamma ranar Alhamis, bayan an sami rahoton cewa an sace yaron kuma masu […]

Hukumar  tsaron ta farin kaya (DSS) ta samu nasarar ceto wani yaro mai shekaru biyar, mai suna Muhammad Haruna, daga hannun masu garkuwa da mutane a Kauyen Danzaki, karamar hukumar Gezawa.

An gudanar da aikin ceton ne da misalin ƙarfe 7:40 na yamma ranar Alhamis, bayan an sami rahoton cewa an sace yaron kuma masu garkuwar suna neman miliyan goma sha biyar a matsayin kudin fansa.

A yayin aikin, jami’an DSS sun cafke Aminu Mukhtar mai shekaru 20, wanda ake zargin mai garkuwa da mutane ne, a lokacin da ya ke tattaunawa da mahaifin yaron ta wayar salula don neman kudin fansa.

Mukhtar ya amsa cewa shi ne ya sace yaron domin neman kuɗin fansa.

Hukumar DSS ta ci gaba da kira ga al’umma da su rika bayar da rahoton duk wani abu da suka lura da shi domin taimakawa wajen yakar garkuwa da yara da kuma tabbatar da tsaron su.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai