Ƙaramar Ministar kwadagon Najeriya Nkeiruka Onyejeocha ta yi murabus daga muƙaminta.
Ta sanar da murabus ɗin nata ne a shafinta na X, inda ta miƙa godiyarta ga shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ya bata dama ta yi aiki da gwamnatinsa.
Ta bayyana ajiye muƙamin nata a matsayin matakin rufe wani gagarumin babi na rayuwarta a matsayinta na ma’aikaciyar gwamnati, kuma ta bayyana burinta na ci gaba aiki tuƙuru wajen ciyar da Najeriya gaba.
Shugaba Tinubu ne ya shaida wa duka masu riƙe da muƙaman siyasa cewa idan suna da burin tsayawa takara a 2027 to su ajiye muƙamansu nan da 31 ga watan Maris 2026, yadda komai zai tafi daidai babu cuta babu cutarwa.

